+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «لا يَقُلْ أحدُكم: اللهم اغفِرْ لي إن شِئْتَ، اللهم ارحمني إن شِئْتَ، لِيَعْزِمِ المسألةَ، فإن الله لا مُكْرِهَ له». ولمسلم: «وَلْيُعَظِّمِ الرَّغْبَةَ، فإن الله لا يَتَعَاظَمُه شيءٌ أعطاه».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi zuwa ga Annabi: "Kada Dayanku ya ce: Ya Ubangiji kayi mun gafara in kaga dama, Allahumma kaji kaina inkaga dama, kawai ya yanke kai tsaye a Addu'ar don babu mai Tilastawa Allah" kuma a riwayar Muslim kuwa: "To ya girmama Bukatar, domin Allah babu abinda aka kambama nemansa a wajensa face ya bada shi"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

kuma yayin da baki dayan bayi Mabukata ne zuwa ga Allah, kuma Allah shi ne Mawadaci kuma abin godiya kuma Mai aikata abinda yake so, sai Annab ya hana duk wanda yai niyyar yin Addu'a ya danfara neman gafarara da jinkai daga Allah da ganin dama, kuma ya Umarce shi da yankewa kai tsaye da nema banda wani danfarawa; domin hakan yana nuna cewa Allah akwai abunda yake wahalar da shi cikin bukatun bayinsa, ko kuma yana takura da biyan wata bukatarsu, kuma wannan ya sabawa gaskiya, kamar yadda wannan yake nuni da gajiyawar bawa da neman bukata da kuma wadatarsa ga barin Ubangijinsa, kuma shi bawa baya wadatuwa daga Ubangijinsa koda kuwa dai dai da kiftawar Ido, kuma wannan yana kore bukatuwar da take itace ruhin Ibdar Addu'a ma, domin bada zabi bai dace da Allah ba, don babu wanda ya isa ya tilastawa Allah yin wani abu, Sannan kuma Annabi yayi marni ga Mai Addu'a da nacewa a cikin Addu'a, kuma ya roki Allah abinda ya so na Alkairi komai girmansa kuma komai kankantarsa; domin cewa Allah babu abinda yake yi masa Wahala idan yai nufin bayar da shi, kuma babu abinda yake yi masa girma na tambaya; sabida shi ne mamallakin Duniya da lahira, kuma shi ne Mai gudanar da komai nasu, kuma shi Mai iko ne akan komai.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Asami الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin