+ -

عَنْ أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لاَ تَسُبُّوا الرِّيحَ، فَإِذَا رَأَيْتُمْ مَا تَكْرَهُونَ فَقُولُوا: اللَّهُمَّ إِنَّا نَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ هَذِهِ الرِّيحِ وَخَيْرِ مَا فِيهَا وَخَيْرِ مَا أُمِرَتْ بِهِ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ هَذِهِ الرِّيحِ وَشَرِّ مَا فِيهَا وَشَرِّ مَا أُمِرَتْ بِهِ».

[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 2252]
المزيــد ...

Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Kada ku zagi Iska, idan kuka ga abinda ba kwa so to kuce: Ya Allah mu muna roƙonKa daga alherin wannan iskar, da alherin abinda ke cikinta, da alherin abinda aka umarce ta da shi, kuma muna neman tsarinKa daga sharrin wannan iskar, da kuma sharrin abinda ke cikinta, da kuma sharrin abinda aka umarce ta da shi".

[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 2252]

Bayani

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani da a zagi ko tsinewa iska, domin ita abar umarta ce daga Mahaliccinta, tana zuwa da rahama da kuma azaba, aibanta ta aibanta Allah ne Mahaliccinta, da fushi akan hukuncinSa, sannan tsira da amincn Allah su tabbata agare shi ya shiryar zuwa komawa ga Allah Mahaliccinta da roƙonSa daga alherinta da alherin abinda ke cikinta da alherin abinda aka aikota da shi, kamar zuwanta da ruwa da ɗaukar abinci (wata madatta ce da take ƙarfafa jikin mutum ko dabba) da makancinsa, da kuma neman tsarin Allah daga sharrinta da sharrin abinda ke cikinta da kuma sharrin abinda aka aikota da shi, kamar bata tsirrai da bishiyoyi da kashe dabbobi da rusa gine-gine da makamancinsa, kuma a cikn rokon Allah akwai tabbatar da ubudiyya ga Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga zagin iska; domin cewa ita halitta ce abar juyawa sai zagin ya koma zuwa ga Mahaliccinta kuma Mai jujjuya al'amuranta, kuma zagin tawaya ne a cikin tauhidi.
  2. Komawa zuwa ga Allah da neman tsari da Shi daga sharrin abinda Ya halitta.
  3. Iska tana kasancewa abar umarta da alheri, kuma tana kasancewa abar umarta da sharri.
  4. Ibnu Baaz ya ce: Zagin iska yana daga jumlar saɓo; domin ita abar halitta ce abar jujjuya al'amuranta ne, ana aikota da alheri da kuma sharri; saboda haka zaginta ba ya halatta, kuma ba'a cewa: Allah Ya tsinewa iska, ko Allah Ya kashe iska, ko kada Allah Ya yi albarka a cikin wannan iskar, ko abinda ke kama da haka, kai mumini ya yi aiki da abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  5. Ana ƙiyasta abinda ya rataya da zafi da sanyi da rana da ƙura da wanin hakan daga abinda yake shi daga halittar Allah ne da tasarrufinSa, akan iska a cikin haramcin zagi da cin mutunci.