عن عائشة رضي الله عنها قالت:
سَأَلَ أُنَاسٌ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْكُهَّانِ، فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَيْسُوا بِشَيْءٍ» قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، فَإِنَّهُمْ يُحَدِّثُونَ أَحْيَانًا بِالشَّيْءِ يَكُونُ حَقًّا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تِلْكَ الْكَلِمَةُ مِنَ الْحَقِّ يَخْطَفُهَا الْجِنِّيُّ فَيَقُرُّهَا فِي أُذُنِ وَلِيِّهِ قَرَّ الدَّجَاجَةِ، فَيَخْلِطُونَ فِيهَا أَكْثَرَ مِنْ مِائَةِ كَذْبَةٍ».

[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Wasu mutane sun tambayi Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da bokaye, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Su ba komai ba ne". Suka ce: Ya Ma’aikin Allah; Wani lokacin suna ba da labari sai kuma abin ya zama gaske. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari.

Ingantacce ne - Buhari ne ya rawaito shi

Bayani

An tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da waɗanda suke ba da labarin abin da zai faru nan gaba na gaibu, sai ya ce: Kada ku kula su, kada ku saurari maganarsu, kada ku shiga al’amarinsu.
Sai suka ce: Maganarsu tana daidai da abin da ya faru a wani lokaci, kamar a ce su ba da labarin wani abu na gaibu zai faru a wata kaza a rana kaza, sai kuma ya faru kamar yadda suka faɗa.
Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Aljanu suna sato abin da suke ji ne na labarun sama, sai su sauko da shi zuwa ga abokan hulɗarsu cikin bokaye, sai su ba su labarin abin da suka ji, sannan sai shi bokan ya ƙara ƙarya ɗari a kan wannan labarin da ya ji daga sama.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An hana a gasgata bokaye, kuma abin da suke faɗa ƙarya ne, kuma ƙagaggen [zance ne] ko da wani lokacin ya zama gaskiya.
  2. An tsare sama daga shaiɗanu da aiko Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da su ji wani abu na wahayi ko waninsa, sai dai wanda ya saci magana ya kuma tsira daga tauraron [harbosu].
  3. Aljanu suna da abokan hulɗarsu cikin mutane