عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«من اقتبَسَ علْمًا مِنَ النُّجُومِ اقْتبَسَ شُعبَة مِن السِّحرِ، زادَ ما زادَ».
[صحيح] - [رواه أبو داود وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 3905]
المزيــد ...
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 3905]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana duk wanda ya koyi, ya samu wani tsagi na ilimin taurari da buruji da kuma kafa dalili da motsinsu da shigarsu da fitarsu a kan abin da zai faru a bayan ƙasa na mutuwar wane, ko rayuwarsa, ko rashin lafiyarsa, da makamancin haka cikin abinda zai faru nan gaba, to, haƙiƙa ya koyi wani tsagi na sihiri, kuma duk lokacin da mutum ya ƙara wannan ilimin, to, ya ƙara asiri [tsafi] ne.