عَنْ أَبِي حُمَيْدٍ أَوْ عَنْ أَبِي أُسَيْدٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمُ الْمَسْجِدَ فَلْيَقُلِ: اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ، وَإِذَا خَرَجَ فَلْيَقُلِ: اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 713]
المزيــد ...
Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 713]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da al'ummarsa addu'ar da ake faɗa a yayin shiga masallaci: (Ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarKa), sai ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sawwaka masa hanyoyin rahamarSa, idan ya yi nufin fita, to, ya ce: (Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa), sai ya roƙi Allah daga falalarSa da ƙarin kyautatawarSa daga arziki na halal.