عن بريدة بن الحصيب رضي الله عنه أنه قال:
بَكِّرُوا بِصَلَاةِ الْعَصْرِ، فَإِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ تَرَكَ صَلَاةَ الْعَصْرِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 553]
المزيــد ...
Daga Abu Buraidah Ɗan Husaib, Allah ya yarda da shi ya ce:
Ku gaggauta sallar La’asar a kan lokaci, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 553]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsawatar a kan jinkirta sallar La’asar daga lokacinta da gangan, kuma duk wanda ya yi hakan, to, aikinsa ya lalace, ya tafi kawai a watse.