+ -

عَنْ ‌مَحْمُودِ بْنِ لَبِيدٍ رضي الله عنه:
أَنَّ ‌عُثْمَانَ بْنَ عَفَّانَ أَرَادَ بِنَاءَ الْمَسْجِدِ فَكَرِهَ النَّاسُ ذَلِكَ، وَأَحَبُّوا أَنْ يَدَعَهُ عَلَى هَيْئَتِهِ، فَقَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ بَنَى مَسْجِدًا لِلهِ بَنَى اللهُ لَهُ فِي الْجَنَّةِ مِثْلَهُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 533]
المزيــد ...

Daga Mahmud ɗan Labid - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Usman ɗan Affan ya yi nufin gina masallaci sai mutane suka ƙi hakan, suka so ya bar shi a kan yadda yake, sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gina masallaci saboda Allah; Allah Zai gina masa kwatankwacinsa a cikin aljanna".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 533]

Bayani

Usman Dan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya yi nufin sake gina masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a tsari mafi kyau daga gininsa na farko, sai mutane suka ƙi hakan; saboda abin da ke cikin yin hakan na canja ginin masallacin daga yananyin gininsa a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, masallacin ya kasance an gina shi da tubali, rufinsa kuma ya kasance na azara, sai dai Usman ya yi nufin ya gina shi da duwatsu da sumunti, sai Usman - Allah Ya yarda da shi - ya ba su labarin cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Wanda ya gina masallaci don neman yardarSa - Maɗaukakin sarki, ba don riya ko jiyarwa ba, Allah zai masa sakayya da mafifici daga jinsin aikinsa, wannan sakamakon shi ne ginawar Allah gida kwatankacinsa a aljanna.

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Tagalog Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa a kan gina masallatai da falalar hakan.
  2. Kara girman masallaci da sabunta shi ya shiga falalar ginin.
  3. Muhimmancin tsarkake niyya saboda Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkanin ayyuka.