عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«صَلَاةٌ فِي مَسْجِدِي هَذَا خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ صَلَاةٍ فِيمَا سِوَاهُ إِلَّا الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1190]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1190]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar sallah a masallacinsa, kuma cewa shi yafi yawan lada daga sallah dubu a cikin waninsa daga masallatan duniya, sai dai Masallaci mai alfarma a Makka, shi ne mafifici daga sallah a cikin masallacinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.