عن قيس بن عاصم رضي الله عنه قال:
أتيتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم أُريدُ الإسلامَ، فأَمَرَني أن أغتَسِلَ بماءٍ وسِدرٍ.
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي] - [سنن أبي داود: 355]
المزيــد ...
Daga Ƙais ɗan Asim - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya.
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 355]
Ƙais ɗan Asim ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali yana son ya musulunta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya yi wanka da ruwa da (ganyan) bishiyar magarya; don kasancewa ganyanta ana amfani da shi a tsafta; don kuma abin da take da shi na ƙamshi mai daɗi.