+ -

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنين رَضيَ اللهُ عنها قَالَتْ:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَسْتَفْتِحُ الصَّلَاةَ بِالتَّكْبِيرِ، وَالقِرَاءَةِ، بِـ الحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ العَالَمِينَ، وَكَانَ إِذَا رَكَعَ لَمْ يُشْخِصْ رَأْسَهُ وَلَمْ يُصَوِّبْهُ، وَلَكِنْ بَيْنَ ذَلِكَ، وَكَانَ إِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ مِنَ الرُّكُوعِ لَمْ يَسْجُدْ حَتَّى يَسْتَوِيَ قَائِمًا، وَكَانَ إِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ مِنَ السَّجْدَةِ لَمْ يَسْجُدْ حَتَّى يَسْتَوِيَ جَالِسًا، وَكَانَ يَقُولُ فِي كُلِّ رَكْعَتَيْنِ التَّحِيَّةَ، وَكَانَ يَفْرِشُ رِجْلَهُ اليُسْرَى وَيَنْصِبُ رِجْلَهُ اليُمْنَى، وَكَانَ يَنْهَى عَنْ عُقْبَةِ الشَّيْطَانِ، وَيَنْهَى أَنْ يَفْتَرِشَ الرَّجُلُ ذِرَاعَيْهِ افْتِرَاشَ السَّبُعِ، وَكَانَ يَخْتِمُ الصَّلَاةَ بِالتَّسْلِيمِ.

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 498]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗe sallah da kabbara, da kuma karatu, da (faɗar) Alhamdu lillahi rabbil aalamina (Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai), ya kasance idan ya yi ruku`u ba ya ɗago kansa, ba kuma ya miƙar da shi saidai tsaka-tsaki, ya kasance idan ya ɗago kansa daga ruku`i ba ya yin sujjada, har sai ya daidaita a tsaye, ya kuma kasance idan ya ɗago kansa daga sujjada, ba ya kuma sujjada har sai ya daidaita a zaune, ya kasance yana yin tahiya a bayan kowace raka`a biyu, ya kasance yana shimfiɗa ƙafar sa ta hagu ya kuma kafe ƙafar sa ta dama, ya kasance yana yin hani gameda irin zaman shaiɗan. sannan yana yin hani mutum ya shimfiɗa hannayen sa guda biyu irin shimfiɗawar namun daji, ya kasance yana rufe sallar da yin sallama.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 498]

Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta yi bayanin sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana buɗe sallarsa da kabbarara harama, sai ya ce: «Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)», kuma yana buɗe karatu da Suratul Fatiha: «Alhamdu lillahi rabbil aalamin (Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai)...». Ya kasance idan ya yi ruku'u bayan tsayuwa, ba ya ɗaga kansa sama kuma ba ya sunkuyar da shi a lokacin ruku'u, kawai yana maida shi daidai wa daida, idan ya ɗago kansa daga ruku'u sai ya tsayu a tsaye kafin ya yi sujjada, idan ya ɗaga kansa daga sujjada ta farko, ba ya sujjada ta biyu har sai ya tabbata a tsaye. Ya kasance yana zama bayan kowanne raka'o’i biyu dan yin tahiya kuma yana cewa: «Attahiyyatu lillahi was salawat waɗɗaibat(Gaishe-gaishe sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkakan ayyuka)...», kuma ya kasance idan ya zauna tsakanin sujjadu biyu ko dan tahiya sai ya shimfiɗa ƙafarsa ta hagu ya zauna a kanta, ya kuma kafa ƙafarsa ta dama. Kuma yana hana mai sallah a cikin sallarsa ya zauna kamar zaman shaiɗan, hakan shi ne ya shimfiɗa ƙafafuwansa akan ƙasa, kuma ya zauna akan ƙarshensu, ko ya ɗanfara mazaunansa a ƙasa ya kafa ƙwaurukansa ya kuma ɗora hannayensa akan ƙasa kamar yadda kare yake yi, ko mai sallah ya shimfiɗa zira'insa ya shimfiɗasu a cikin sujjada kamar yadda namun daji suke yi . Kuma ya kasance yana cika sallarsa da yin sallama: «Assalamu alaikun warahmatullah» daga dama sau ɗaya, ɗayan kuma daga hagu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin wani abu daga cikin siffar sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. Wajabcin kabbarar haramar da take haramta kowace magana da aikin da yake kore maganganun sallah da kuma ayyukanta, kuma wanin wannan sigar (ta Allahu Akbar) ba ta tsayawa matsayinsu dan shiga cikin sallah.
  3. Wajabcin karatun Fatiha.
  4. Wajabcin ruku'u, abin da ya fi a cikinsa shi ne daidaituwa ba tare da ɗagawa, ko sunkuyarwa ba.
  5. Wajabcin ɗagowa daga ruku'u, da kuma wajabcin daidaituwa a cikin tsayuwa a bayansa.
  6. Wajabcin sujjada, da wajabcin ɗagowa daga gareta, da kuma daidaituwa a zaune a bayanta.
  7. Halaccin mai sallah ya shimfiɗa ƙafarsa ta hagu da kafa ta dama a lokacin zama a cikin sallah, amma a cikin tahiyar ƙarshe a cikin sallar da a cikinta akwai tahiyoyi biyu kamar magariba da issha'i to abin da aka shara'anta shine tawarruk, haƙiƙa hadisai da yawa sun zo da hakan.
  8. Hani daga kamanceceniya da shaiɗan a zamansa, hakan shi ne ya zauna akan ƙarshen ƙafafuwansa ya shimfiɗa ƙafafuwansa akan ƙasa, ko ya kafasu ya zauna a tsakaninsu akan ƙasa.
  9. Hani daga kamanceceniya da namun daji a yadda suke shimfiɗa ƙafafuwansu, hakan shi ne mai sallah ya shimfiɗa zira'insa a ƙasa, domin hakan alama ce ta kasala da rauni.
  10. Hani daga kamanceceniya da shaiɗan da kuma dabbobi a cikin ayyukan sallah.
  11. Wajabcin rufe sallah da yin sallama, shi ne yi wa masu sallah mahalarta da waɗanda basa nan, amma salihai addu'a da kuɓuta daga dukkanin sharri.
  12. Wajabcin nutsuwa a cikin sallah.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Yaran Tailand Asami الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin