عن مالك بن الحويرث رضي الله عنه : أنه رأى النبي صلى الله عليه وسلم يصلي، فإذا كان في وِتْرٍ من صلاته لم ينهض حتى يستوي قاعداً.
[صحيح] - [رواه البخاري]
المزيــد ...
Daga Malik Bn Huwairith -Allah ya yarda da shi Lallai cewa Manzon Allah SAW idan ya kasanc a Wuturin Sallarsa baya tashi har sai ya daidaita a zaune
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi]
Ya kasance cikin koyarwar Manzon Alllah SAW idan ya tashi daga Raka'ar farko zuwa ta biyu, da ta Uku zuwa ta Hudu baya tashi har sai ya tabbata a zaune zama takaitacce, sannan ya ya tashi, kuma wannan zaman ana kiransa da zaman Hutawa, kuma haqiqa Adadin Sahabbai da yawa sun rawaito hakan