+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه:
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ دَخَلَ المَسْجِدَ فَدَخَلَ رَجُلٌ، فَصَلَّى، فَسَلَّمَ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَرَدَّ وَقَالَ: «ارْجِعْ فَصَلِّ، فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ»، فَرَجَعَ يُصَلِّي كَمَا صَلَّى، ثُمَّ جَاءَ، فَسَلَّمَ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «ارْجِعْ فَصَلِّ، فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ» ثَلاَثًا، فَقَالَ: وَالَّذِي بَعَثَكَ بِالحَقِّ مَا أُحْسِنُ غَيْرَهُ، فَعَلِّمْنِي، فَقَالَ: «إِذَا قُمْتَ إِلَى الصَّلاَةِ فَكَبِّرْ، ثُمَّ اقْرَأْ مَا تَيَسَّرَ مَعَكَ مِنَ القُرْآنِ، ثُمَّ ارْكَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ رَاكِعًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَعْدِلَ قَائِمًا، ثُمَّ اسْجُدْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ سَاجِدًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ جَالِسًا، وَافْعَلْ ذَلِكَ فِي صَلاَتِكَ كُلِّهَا».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 757]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo, sai ya yi sallah, sannan (ya zo) ya yi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-sai ya amsa masa kuma ya ce: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba", sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo ya yi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Koma ka yi sallah, domin cewa kai baka yi sallah ba" sau uku, sai ya ce: Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan iya yin wacce ta fita ba, to ka koya mini, sai ya ce: "Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka tare da kai na Alkur'ani, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, sannan ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, sannan ka dago har sai ka natsu a zaune, kuma ka aikata hakan acikin sallarka gaba dayanta".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 757]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo a bayansa sai ya yi sallah raka'a biyu da gaggawa, bai nutsu a cikin tsayuwarsa da ruku'unsa da sujjadarsa ba, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lura da shi a cikin sallarsa, sai ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin Ma’aikin Allah yana zaune a gefen masallaci sai ya yi masa sallama, sai ya amsa masa sallamar, kuma ya ce masa: Ka koma ka sake sallarka, domin kai baka yi sallah ba. Sai ya dawo yana sallah da gaggawa kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo sai ya yi sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce masa: Ka koma ka yi sallah; domin kai baka yi sallah ba, ya aikata haka sau uku. Sai mutumin ya ce: Na rantse da wanda Ya aikoka da gaskiya, ba zan iya yin wacce tafi wannan ba to ka koya mini, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbarar harama, sannan ka karanta Fatiha da kuma abinda Allah Ya so ka karanta, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, shi ne ka sanya tafukanka biyu akan gwiwoyinka sai ka miƙar da bayanka ka tabbata dan yin ruku'inka, sannan ka ɗago ka daidaita bayanka har sai ƙasusuwa sun koma mararrabarsu kuma ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, shi ne ka tabbatar da goshi tare da hanci, da hannaye da gwiwoyi da geffan diga-digai akan ƙasa, sannan ka ɗago har sai ka natsu kana zaune tsakanin sujjada biyu, sannan ka aikata hakan a kowace raka'a ta sallarka.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Waɗannan rukunan na sallah, ba sa faɗuwa ba da rafkanuwa ba ba kuma da jahilci ba, saboda dalilin umartar mai sallar da sakewa, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai isu da koyar dashi ba (saida ya sashi ya sake).
  2. Natsuwa rukuni ce daga cikin rukunan sallah.
  3. Nawawi ya ce: A cikinsa cewa wanda ya ɓata wasu wajiban sallah to sallarsa ba ta inganta ba.
  4. Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa akwai sauƙaƙawa ga mai neman sani da kuma jahili da sassauta masa, da bayyanar da masa'alar gare shi da rairaye manufofi, da taƙaitawa a matakinsa akan manyan mihimmai banda wadanda suke cikawa waɗanda halinsa ba zai iya ɗaukar iya kiyayesu da kuma tsayuwa da su ba.
  5. Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa cewa mai bada fatawa idan an tambaye shi game da wani abu, kuma a nan akwai wani abu daban da mai tambayar yake buƙatuwa zuwa gare shi kuma bai tambaye shi ba to an so ga matawar ya faɗa masa shi, kuma wannan ya zama daga nasiha ne ba daga zancen da bai shafe shi ba ne.
  6. Falalar iƙirari da kasawa saboda faɗinsa; "Ba zan iya yin wacce ta fi ta ba to ka koya mini".
  7. Ibnu Hajar ya ce: Kuma a cikinsa akwai horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi, da kuma neman mai neman sani daga malami cewa ya koya masa.
  8. An so yin sallama a lokacin haɗuwa, da kuma wajabcin amsa ta, kuma an so maimaitata idan haɗuwa ta maimaitu koda ba'ajima ba, kuma cewa wajibi ne ya amsa masa a kowane lokaci.