عن جُبَيْرُ بْنُ مُطْعِم رضي الله عنه قال: «سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقرأ في المغرب بِالطُّور».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jubair Dan Mud'im -Allah ya yarda da shi- yace:"Na ji Annabi -tsira da amincin Allah- yana karanta Suratuddur a Sallar Magariba".
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Al'adar Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana tsawaita karatu a sallar Asuba, ya takaita a Magariba, yayi tsakatsaki a sauran sallolin, amma wani lokacin sai ya bar abin daya saba yi don ya nuna halarci yin sabanin abin, kamar yadda ya zo a wannan hadisin cewa shi ya karanta "Waddur" kuma tana daga surorin da ake cewa {Diwalul Mufassal}

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin