عن حُذَيْفَةَ رضي الله عنه:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ بَيْنَ السَّجْدَتَيْنِ: «رَبِّ اغْفِرْ لِي، رَبِّ اغْفِرْ لِي».
[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي وابن ماجه وأحمد] - [سنن ابن ماجه: 897]
المزيــد ...
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi -:
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'.
[Ingantacce ne] - - [سنن ابن ماجه - 897]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a yayin zama a tsakaknin sujjada biyu: Ya Ubangina ka gafarta min, yana maimaita ta.
Ma'anar ya Ubangijina Ka gafarta min: Bawa yana neman daga Ubangijinsa ya shafe masa zunubansa ya suturta aibukansa.