+ -

عَنْ ‌أَبِي الزُّبَيْرِ قَالَ:
كَانَ ‌ابْنُ الزُّبَيْرِ يَقُولُ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ حِينَ يُسَلِّمُ: «لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، ‌وَلَا ‌نَعْبُدُ ‌إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ وَلَهُ الْفَضْلُ وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ» وَقَالَ: «كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُهَلِّلُ بِهِنَّ دُبُرَ كُلِّ صَلَاةٍ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 594]
المزيــد ...

Daga baban Zubair ya ce:
Dan Zubair ya kasance yana cewa a bayan kowacce Sallah idan ya yi sallama: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki na Sa ne, kuma godiya ta Sa ce, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ba dabara ba ƙarfi sai da Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, Shi Ya ke da ni’ima da falala, Shi ke da kyawawan yabo, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsarkake addini gare shi, ko da kafirai sun ƙi. Ya kuma ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 594]

Bayani

Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana HAILALA bayan ya sallame daga kowacce sallah ta farilla da wannan zikirin mai girma, Ma’anarsa ita ce:
"Babu abin bautawa sai Allah"; Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah.
"Shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya": Wato babu wanda yake tarayya da Shi a Allantaka [ cancantar bauta ] ko a rububiyya [ kasancewarSa Mahalicci, Mai azurtawa, Mai rayawa, Mai matarwa ] ko kuma a sunaye da siffofinSa.
"Mulki na sa ne": Wato; Shi Ya ke da cikakken mulki wanda ya game komai, mulkin sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu.
"Godiya ta sa ce": Wato shi ne wanda ya siffantu da cikakkiyar cika, wanda ake yabonSa da cika saboda so da girmawa a kowanne lokaci, na farin ciki da na damuwa.
"Shi mai iko ne a kan komai": IkonSa cikakken iko ne ta kowacce fuska, babu abin da yake gagararsa, babu wani al’amari da zai gagare shi.
"Ba dabara ba ƙarfi sai da yin Allah": Wato babu canji daga wani hali zuwa wani halin, ko daga saɓon Allah zuwa ga baiyayyarSa, haka babu ƙarfi, sai da Allah wanda Shi ne Mai taimako, kuma Wanda ake dogara da Shi.
"Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi": karfafawa ce a kan ma’anar Allantaka da kuma kore shirka, da cewa babu wanda ya cancanci bauta in ba Shi ba.
"Ni’ima ta Sa ce da falala": Shi ne wanda ya halicci ni’imomi kuma yake mallakarsu, yake kuma ba da su ga wanda Ya so cikin bayinSa.
"Kyakkyawan yabo nasa ne": A bisa zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa da Ni’imominSa a kowanne lokaci.
"Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsantsanta addini a gareShi": Wato, muna masu Tauhidi, babu riya, kuma babu jiyarwa a kan biyayya ga Allah.
"Koda kafirai sun ƙi": Wato muna masu tabbatuwa a kan Tauhidi da bauta masa ko da kafirai sun ƙi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so kulawada da wannan zikirin bayan kowacce sallah ta farilla.
  2. Musulmi yana ji da addininsa, kuma yana bayyana ayyukan addininsa, ko da kafirai sun ƙi.
  3. Idan a cikin Hadisi aka ce: "bayan sallah", to, idan abin da a ka ce a Hadisin zikiri ne, to, asali ana nufin bayan sallama, idan kuma addu’a ce, to, ana nufin kafin sallama.
Kari