عن أبي هريرة رضي الله عنه: أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«لَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ مَقَابِرَ، إِنَّ الشَّيْطَانَ يَنْفِرُ مِنَ الْبَيْتِ الَّذِي تُقْرَأُ فِيهِ سُورَةُ الْبَقَرَةِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 780]
المزيــد ...

Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [Sahih Muslim - 780]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah, sai su zama kamar maƙabartu, da ba a sallah a cikinsu.
Sannan sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labarin shaiɗan yana ficewa daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ana so a yawaita ibada da Sallolin Nafila a gidaje.
  2. Ba ya halatta yin Sallah a maƙabarta, domin hakan hanya ce daga hanyoyin shirka da wuce iyaka ga masu su, in banda sallar Janaza.
  3. Hanin yin Sallah a inda akwai kabari, ya tabbata a wurin Sahabbai, saboda haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana a sanya gidaje kamar maƙabartu, waɗanda su ba a Sallah a cikinsu.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (62)