عن أبي الدرداء رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ حَفِظَ عَشْرَ آيَاتٍ مِنْ أَوَّلِ سُورَةِ الكَهْفِ، عُصِمَ مِنَ الدَّجَّالِ». وفي رواية: «مِنْ آخِرِ سُورَةِ الكَهْف».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 809]
المزيــد ...
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 809]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya haddace ayoyi goma a zahirin zuciya (hadda) daga farkon Suratul Kahf za'a tsare shi za'a kare shi daga fitinar Masihul Dajjal wanda zai fito a ƙarshen zamani kuma zai yi da'awar Uluhiyya (Allantaka), kuma fitinarsa ita ce mafi girman fitinar da za ta kasance a kan ƙasa tun lokacin da aka halicci (annabi) Adam har zuwa tashin alƙiyama; saboda abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Zai tabbatar masa daga sashin al'amura masu saɓa hankali waɗanda zai fitini wanda ya bi shi, hakan domin cewa farkon Suratul Kahf a cikinta akwai abubuwan mamaki da ayoyi abinda yake yafi girma daga abinda Dujal zai fitini mutane a cikinsa, wanda ya yi tuntuntuni to ba za'a fitina shi da Dujjal ba. A cikin wata riwayar: Ayoyi goma daga ƙarshen surar daga faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Shin waɗanda suka kafirta suna zatan zasu riƙi...}.