عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«لَأَنْ أَقُولَ: سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَاللهُ أَكْبَرُ، أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمْسُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2695]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma.
Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2695]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labari cewa anbaton Allah (Zikiri) da waɗannan kalmomi masu girma, shi ya fi duniya da abin da yake cikinta, su ne:
"Tsarki ya tabbata ga Allah": Tsarke Allah ne daga dukkan tawaya.
"Godiya ta tabbata ga Allah": Yabon Allah ne da siffofinSa na Kamala tare da sonSa da kuma girmamaShi.
"Babu abin bautawa sai Allah": Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah.
Allah ne mafi girma; Mafi girma da ɗaukaka a kan komai.