عن جابر رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«أَفْضَلُ الذِّكْرِ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَفْضَلُ الدُّعَاءِ: الْحَمْدُ لِلهِ».
[حسن] - [رواه الترمذي والنسائي في الكبرى وابن ماجه] - [سنن الترمذي: 3383]
المزيــد ...
Daga Jabir -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:
"Mafificin zikiri: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mafificiyar addu'a: Godiya ta tabbata ga Allah".
[Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 3383]
Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa mafificin zikiri: "La ilaha illal lahu" Ma'anarta babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa mafificiyar addu'a godiya ta tabbata ga Allah; shi ne ikirari da cewa mai ni'imtarwa Shi ne Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, wanda ya cancanci cikakkiyar siffa mai kyau.