+ -

كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِذَا كَبَّرَ فِي الصَّلَاةِ، سَكَتَ هُنَيَّةً قَبْلَ أَنْ يَقْرَأَ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ بِأَبِي أَنْتَ وَأُمِّي أَرَأَيْتَ سُكُوتَكَ بَيْنَ التَّكْبِيرِ وَالْقِرَاءَةِ، مَا تَقُولُ؟ قَالَ «أَقُولُ: @اللهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ*، اللهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، اللهُمَّ اغْسِلْنِي مِنْ خَطَايَايَ بِالثَّلْجِ وَالْمَاءِ وَالْبَرَدِ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi kabbarar sallah yana yin shiru kaɗan kafin ya karanta fatiha, yana buɗe sallarsa da wasu daga addu'o'i a cikinta, daga abinda ya zo daga waɗannan addu'o'in faɗinsa: "Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti, ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwa da ƙanƙara da ruwa mai tsananin sanyi". Shi yana roƙon Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya nisantar da tsakaninsa da kurakurai da kada ya faɗa cikinsu, nisantarwa ta inda gamuwa ba zata ƙara faruwa tare da shi ba, kamar yadda babu haɗuwa tsakanin mahudar rana da mafaɗarta har abada, idan kuma ya faɗa cikinsu to Ya tsaftace su Ya kawar da su kamar yadda ake kawar da datti daga farin tufa, kuma Ya wanke shi daga kurakuransa Ya sanyaya horuwarsu da zafinsu, da waɗannan masu tsaftacewar masu sanyi: Ruwa, da kankara, da sanyi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami السويدية الأمهرية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Boye addu'ar buɗe sallah koda sallar ta kasance ta karatun bayyana ne.
  2. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan sanin halayen Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a motsinsa da shirunsa.
  3. Wasu sigogin daban sun zo na addu'ar buɗe sallah, abinda ya fi shi ne mutum ya bibiyi addu'o'in buɗe sallah da suka zo, kuma tabbatattu daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma ya zo da wannan.