عَنْ كَعْبِ بْنِ عُجْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مُعَقِّبَاتٌ لَا يَخِيبُ قَائِلُهُنَّ -أَوْ فَاعِلُهُنَّ- دُبُرَ كُلِّ صَلَاةٍ مَكْتُوبَةٍ، ثَلَاثٌ وَثَلَاثُونَ تَسْبِيحَةً، وَثَلَاثٌ وَثَلَاثُونَ تَحْمِيدَةً، وَأَرْبَعٌ وَثَلَاثُونَ تَكْبِيرَةً».

[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Ka'ab dan Ujrah - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da wasu zikiran da mai fadainsu ba ya asara kuma ba ya tabewa, kai yana da ladan wadannan kalmomin, kuma sashinsu yana zuwa bayan sashi, ana fadarsu a bayan sallolin farilla, su ne:
"Tsarki ya tabbata ga Allah" sau talatin da uku, wato tsarkakeshi - Madaukakin sarki - daga dukkanin tawaya.
"Godiya ta tabbata ga Allah" sau talatin da uku, ita ce siffanta Allah da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamaShi.
"Allah ne Mafi girma" sau talatin da hudu, Allah ne Mafi girmamawa Mafi buwaya daga dukkan komai.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar tasbihi da tahmidi da kabbara, su ne wanzajju nagartattu.