+ -

عَن أَبي مُوْسى الأَشْعريِّ رضي الله عنه قال: قال رسولُ اللهِ صلى اللهُ عليه وسلم:
«مَثَلُ الْمُؤْمِنِ الَّذِي يَقْرَأُ الْقُرْآنَ كَمَثَلِ الْأُتْرُجَّةِ، رِيحُهَا طَيِّبٌ وَطَعْمُهَا طَيِّبٌ، وَمَثَلُ الْمُؤْمِنِ الَّذِي لَا يَقْرَأُ الْقُرْآنَ كَمَثَلِ التَّمْرَةِ، لَا رِيحَ لَهَا وَطَعْمُهَا حُلْوٌ، وَمَثَلُ الْمُنَافِقِ الَّذِي يَقْرَأُ الْقُرْآنَ مَثَلُ الرَّيْحَانَةِ، رِيحُهَا طَيِّبٌ وَطَعْمُهَا مُرٌّ، وَمَثَلُ الْمُنَافِقِ الَّذِي لَا يَقْرَأُ الْقُرْآنَ كَمَثَلِ الْحَنْظَلَةِ، لَيْسَ لَهَا رِيحٌ وَطَعْمُهَا مُرٌّ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5427]
المزيــد ...

Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kwatankwacin muminin da yake karanta AlKur'ani kamar gawasa ne, kanshinta mai dadi ne, kuma dandanonta mai dadi ne, kuma kwatankwacin muminin da ba ya karanta AlKur'ani kamar dabino ne ba shi da kanshi amma dandanonsa ma zaki ne, kuma kwatankwacin munafikin da yake karanta AlKurani kamar nana ne kanshinsa mai dadi ne amma dandanonta mai daci ne, kuma kwatankawacin munafikin da ba ya karanta AlKura'ni kwatankwacin guna ce ba ta da kanshi, kuma dandanonta mai daci ne".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5427]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana karkasuwar mutane a karatun AlKur'ani da amfanuwa da shi:
Kashi na farko: Muminin da yake karanta AlKur'ani kuma yake amfanuwa da shi, to shi kamar gawasa ne, mai dadin dandano da kanshi, da kyakkyawan launi, kuma amfaninsa mai yawa ne, shi yana aiki da abinda ya karanta, kuma yana amfanar bayin Allah.
Kashi na biyu: Muminin da ba ya karanta AlKur'ani, to shi kamar dabino ne, dandanonsa mai zaki ne, kuma ba shi da kanshi, to zuciyarsa mai tattare da imani ce kamar tattarowar dabino akan zaki a dandanonsa da cikinsa, da rashin bayyanar kanshi gare shi wanda mutane za su shaka; Saboda rashin bayyanar karatu daga gare shi wanda mutane za su ji dadin jinsa.
Na uku: Munafikin da yake karanta AlKur'ani: To shi kamar nana ne, tana da dadin kanshi kuma dandanonta mai daci ne, ta inda bai gyara zuciyarsa da imani ba, kuma bai yi aiki da AlKur'ani ba, kuma yana bayyana ga mutane cewa shi muminine, to kanshinta mai dadi yana kama da karatunsa, dandanonta mai daci kuma yana kama da kafircinsa.
Na hudu: Munafikin da ba ya karanta AlKur'ani, to shi kamar guna ne, ta inda ita ba ta da kanshi, da kuma dacin dandanonta, to rashin kanshinta ya yi kama da rashin kanshinsa; Saboda rashin karatunsa, kuma dacin dandanonta ya yi kama da dacin kafircinsa, cikinsa ya kadaita daga imani, zahirinsa kuma babu amfani a cikinsa, kai shi mai cutarwa ne.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin falalar mai dauke da AlKur'ani mai aiki da shi.
  2. Daga hanyoyin koyarwa akwai buga misalai; Dan kusanto da fahimta.
  3. Yana kamata ga musulmi ya zama yana da wani wuridai da yake yi kullum na karatun littafin Allah - Madaukakin sarki -.