+ -

عن عثمان رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«خَيْرُكُمْ مَنْ تَعَلَّمَ الْقُرْآنَ وَعَلَّمَهُ».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 5027]
المزيــد ...

Daga Usman Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya ce:
"Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi".

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5027]

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin mafi falalar Musulmai, wanda kuma yake ƙololuwar daraja a wurin Allah shi ne, wanda ya koyi Alƙur’ani, karatun da hadda da rerawa da fahimta da Tafsir. Ya kuma sanar da wani abin da yake wurinsa na iliman Alkur’ani (Ulumul Qur’an) tare da aiki da shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin matsayin Alkur’ani, kuma shi ne mafificin zance; domin shi zancen Allah ne.
  2. Mafificin masu koyo shi ne wanda yake sanar da waninsa, ba wai wanda ya taƙaitu a kansa kawai ba.
  3. Koyon Alkur’ani da koyar da shi ya ƙunshi karatu da [sanin] ma’anoni da Hukunce Hukunce.