عَنِ الْبَرَاءِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَا مِنْ مُسْلِمَيْنِ يَلْتَقِيَانِ فَيَتَصَافَحَانِ إِلَّا غُفِرَ لَهُمَا قَبْلَ أَنْ يَفْتَرِقَا».
[صحيح بمجموع طرقه] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 5212]
المزيــد ...
Daga Bara'u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -:
"Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu".
- - [سنن أبي داود - 5212]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari: Cewa babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu a wata hanya da makamancinta ɗayansu ya yi wa ɗayan sallama, gaisuwa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu da jikkuna ko da gama gaisuwar.