عَنْ سُلَيْمَانَ بْنِ صُرَدٍ رضي الله عنه قَالَ:
كُنْتُ جَالِسًا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَرَجُلاَنِ يَسْتَبَّانِ، فَأَحَدُهُمَا احْمَرَّ وَجْهُهُ، وَانْتَفَخَتْ أَوْدَاجُهُ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي لَأَعْلَمُ كَلِمَةً لَوْ قَالَهَا ذَهَبَ عَنْهُ مَا يَجِدُ، لَوْ قَالَ: أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ، ذَهَبَ عَنْهُ مَا يَجِدُ» فَقَالُوا لَهُ: إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «تَعَوَّذْ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ»، فَقَالَ: وَهَلْ بِي جُنُونٌ؟
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3282]
المزيــد ...
Daga Salaiman Bin Surad - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kasance ina zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali wasu mutane biyu suna zage-zage, ɗayansu fuskarsa ta yi jā, jijiyoyinsa sun buɗe, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi" sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan", sai ya ce: Shin ni ina da hauka ne?
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3282]
wasu mutane biyu sun yi zage-zage a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali fuskar ɗayansu ta yi jā, jijiyoyinsa da suka kewaye wuyansa sun kunbura.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na san kalmar da wannan mai fushin zai faɗeta da fushin ya tafi daga gare shi, da zai ce: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa.
Sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan.
Sai ya ce: Shin ni mahaukaci ne? ya yi zatan cewa ba mai neman tsari daga Shaiɗan sai wanda yake da hauka.