عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَلاَ أُنَبِّئُكُمْ بِخَيْرِ أَعْمَالِكُمْ، وَأَزْكَاهَا عِنْدَ مَلِيكِكُمْ، وَأَرْفَعِهَا فِي دَرَجَاتِكُمْ وَخَيْرٌ لَكُمْ مِنْ إِنْفَاقِ الذَّهَبِ وَالوَرِقِ، وَخَيْرٌ لَكُمْ مِنْ أَنْ تَلْقَوْا عَدُوَّكُمْ فَتَضْرِبُوا أَعْنَاقَهُمْ وَيَضْرِبُوا أَعْنَاقَكُمْ؟» قَالُوا: بَلَى. قَالَ: «ذِكْرُ اللهِ تَعَالَى».
[صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 3377]
المزيــد ...
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku kuma mafi alheri agareku daga ciyar da zinari da azirfa, kuma mafi alheri agareku daga ku haɗu da maƙiyanku ku daki wuyan su, suma su daki wuyan ku?" suka ce: Eh. Ya ce: "Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 3377]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: .
Shin kuna son in baku labari ? In sanar da ku da mafificin ayyukanku, kuma mafi ɗaukakarsu, mafi ƙaruwarsu, mafi tsarkinsu, mafi tsaf-tsaf ɗinsu a wurin Allah Mamallaki - Mai girma da ɗaukaka -? .
kuma mafi ɗaukakarsu a cikin masaukanku a aljanna?
kuma mafi alheri gareku daga sadaka da zinare da azirfa?
Kuma mafi alheri a gareku daga ku haɗu da kafirai dan yaƙi, sai ku daki wuyansu, su daki wuyanku ?
Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan.
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkan lokuta da kuma dukkan siffofi da halaye.