عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَلَا أَدُلُّكُمْ عَلَى مَا يَمْحُو اللهُ بِهِ الْخَطَايَا، وَيَرْفَعُ بِهِ الدَّرَجَاتِ؟» قَالُوا بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ قَالَ: «إِسْبَاغُ الْوُضُوءِ عَلَى الْمَكَارِهِ، وَكَثْرَةُ الْخُطَا إِلَى الْمَسَاجِدِ، وَانْتِظَارُ الصَّلَاةِ بَعْدَ الصَّلَاةِ، فَذَلِكُمُ الرِّبَاطُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 251]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka darajoji da shi?" Suka ce: Na'am, ya Manzon Allah, ya ce: "Cika alwala a lokutan da ake ƙi, da yawan takawa zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wadannan su ne shi ne zaman dako".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 251]
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa shin suna son ya nuna musu wasu ayyukan da za su zama sababi a gafarta zunubai, da shafesu daga littatttafan (mala'iku) masu kiyayewa, da ɗaukakar darajoji a cikin aljanna?
Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan. Ya ce:
Na farko: Gamewa da cika alwala a wahala; kamar (lokacin) sanyi da ƙarancin ruwa, da raɗaɗin jiki, da ruwan zafi.
Na biyu: Yawan takawa - shi ne abinda ke tsakanin diga-digai biyu - zuwa masallatai, ta nisan gida da Masallacin, da yawan maimaita zuwa Masallaci.
Na uku: Jiran lokacin sallah, da ratayar zuciya ga sallar, da yin tanadi gareta, da zama gareta a cikin masallatai dan jiran jama'a, idan ya sallace ta to ya jira wata sallar ta gaba a nan inda ya yi sallah.
Sannan tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa waɗannan al'amuran su ne zaman dako na haƙiƙa; domin suna toshe hanyoyin Shaiɗan ga mutum, kuma suna rinjayar da son rai, kuma suna hana rai daga shiga waswasi, sai rundunar Allah su rinjayi rundunar Shaiɗan da su; Hakan shi ne jihadi mafi girma, sai suka zama a matsayin zaman dako a kafofin maƙiya.