+ -

عَنْ حَارِثَةَ بْنِ وَهْبٍ الخُزَاعِيِّ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِأَهْلِ الجَنَّةِ؟ كُلُّ ضَعِيفٍ مُتَضَعِّفٍ، لَوْ أَقْسَمَ عَلَى اللَّهِ لَأَبَرَّهُ، أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِأَهْلِ النَّارِ: كُلُّ عُتُلٍّ جَوَّاظٍ مُسْتَكْبِرٍ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4918]
المزيــد ...

Daga Harisa ɗan Wahb alKhuza'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da Allah zai kuɓutar da shi, shin ba zan baku labarin 'yan wuta ba? duk mai ƙaton ciki mai kaushin rai mai girman kai".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4918]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin sashin siffofin 'yan aljanna da 'yan wuta.
Mafi yawancin 'yan aljanna sune: "Dukkan mai rauni mai ƙanƙar da kai", wato: Mai ƙanƙan da kai mai ƙanƙanr da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki -, mai ƙasƙantar da kansa gareShi, har takai wasu daga mutane suna raunana shi kuma suna wulaƙanta shi, wannan mai ƙasƙantar da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da zai yi rantsuwa da Allah dan kwaɗayi a cikin karamcin Allah - Maɗaukakin sarki -, da Allah Ya kuɓutar da shi, kuma Ya tabbatar masa da abinda ya yi rantsuwa akansa kuma Ya amsa buƙatarsa da addu'arsa.
Kuma mafi yawancin 'yan wuta su ne: Dukkan "Mai ƙaton ciki" shi ne mai kaushin zuciya, mai bushewar zuciya mai tsananin husuma, ko mai alfasha wanda ba ya jawuwa ga alheri, "Mai yawan girman kai" shi ne mai girman kai, mai yawan ci, mai ƙiba, mai taƙama a tafiyarsa, mai mummunar ɗabi'a, "Mai girman kai" saboda butulcewarsa ga gaskiya, da kuma wulaƙanta waninsa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan siffantuwa da siffofin 'yan aljanna, da kuma gargaɗarwa daga siffofin 'yan wuta.
  2. Kanƙantar da kai yana kasancewa ne ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da umarninSa da haninSa, da jawuwa garesu, kuma yana kasancewa ne ga halitta da rashin yi musu girman kai.
  3. Ibnu Hajar ya ce: Abin nufi cewa mafi yawancin 'yan aljanna sune waɗannan, kamar yadda mafi yawancin 'yan wuta sune ɗaya ɓangaren, bawai abin nufi shi ne gamewa a ɓangarori biyun ba.