عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما مرفوعاً: "العائد في هِبَتِهِ، كالعائد في قَيْئِهِ".
وفي لفظ: "فإن الذى يعود في صدقته: كالكلب يَقِئ ُثم يعود في قيئه".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Mai fasa kyautarsa, kamar mai dawowa ne cikin Amansa" a cikin wani Lafazin kuma: "Domin wanda yake fasa sadakarsa: kamar Karenda yai amai kuma ya dawo yana lashe shi"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Annabi ya buga Misali ne don tsawatarwa daga fasa kyauta da mafi muni sura, ita ce ewa mai fasa kyautarsa, kamar kare ne wanda zai yi Amai sannan ya je ya lashe Amansa, sai ya ci daga abinda yake nuna Munin wannan halin nasa da kuma kaskascinsa, da kuma koma bayan wanda yayi hakan.