عَن أُمِّ الدَّرْدَاءِ وَ أَبِي الدَّرداءِ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ:
«دَعْوَةُ الْمَرْءِ الْمُسْلِمِ لِأَخِيهِ بِظَهْرِ الْغَيْبِ مُسْتَجَابَةٌ، عِنْدَ رَأْسِهِ مَلَكٌ مُوَكَّلٌ كُلَّمَا دَعَا لِأَخِيهِ بِخَيْرٍ، قَالَ الْمَلَكُ الْمُوَكَّلُ بِهِ: آمِينَ وَلَكَ بِمِثْلٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2733]
المزيــد ...
Daga Ummu al-Darda'i da Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbara agare shi - ya kasance yana cewa:
«Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2733]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa musulmi a bayan idon wanda aka yi wa addu'ar abar karɓa ce; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a cikin ikhlasi, kuma lallai cewa a wajen kan mai addu'ar akwai wani Mala'ikan da aka wakilta, a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce; Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin abinda ka roƙa.