+ -

عن عبد الله بن زيد بن عاصم المازني رضي الله عنه قال: (شُكِيَ إلى النبيِّ صلى الله عليه وسلم الرَّجلُ يُخَيَّلُ إِليه أنَّه يَجِد الشَّيء في الصَّلاة، فقال: لا ينصرف حتَّى يَسمعَ صَوتًا، أو يَجِد رِيحًا).
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Zaidu Dan Asim Almaziny -Allah ya yarda da shi- yace: ((An kai kukan Mutumin da yake jin kamar wani abu na sauti a cikinsa a lokacin salla,sai Annabi tsira da amincin Allah yace:kar ka fita daga salla har sai ka ji wata kara,ko ka ji wari)).
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Wannan hadisin kamar yadda Nawawy -Allah rahamshe shi- ya fada yana daga ginshikan musulunci wanda suka ginu kan hukunce-hukunce masu yawa,shi ne ana barin abubuwa a bisa asalin yadda hukuncinsu yake, baza a bar asalin hukunci abu saboda zato ko shakka ba,komai girman shakkar kuwa, indai baa sami tabbas ba, ko zato mafi rinjaye, irin wannan misalan da yawa,don haka indai mutum ya tabbatar yana da tsarki to,sai shakka ta shige shi,to kawai tsarkinsa na nan,tufafi da wuri suma sun shiga cikin wannan hukuncin,abin nufi suna da tsarki har sai an tabbatar da samuwar najasar,haka nan adadin raka'o'in salla, wanda ya tabbatar ya yi raka'a uku,sai yayi shakka game da ta hudu,to asali sai ya dauka ba ta hudun,sai yayi ta hudun ,hakanan wanda yayi shakka game sakin matarsa,to aurensa yana nan har sai ya sami tabbacin sakin,hakanan hukunce-hukunce da yawa wanda a bayyane suke.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili
Manufofin Fassarorin