عَنِ شُرَيْحٍ بنِ هانِئٍ قَالَ:
سَأَلْتُ عَائِشَةَ، قُلْتُ: بِأَيِّ شَيْءٍ كَانَ يَبْدَأُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ بَيْتَهُ؟ قَالَتْ: بِالسِّوَاكِ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 253]
المزيــد ...
Daga Shuraih ɗan Hani'i ya ce:
Na tambayi Nana A'isha, na ce: Da wane abu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yakasance yake farawa idan ya shiga gidansa? ta ce: Da asuwaki.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 253]
Ya kasance daga shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yana farawa da asuwaki idan ya shiga gidansa a kowane lokaci da daddare ko da rana.