عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: إِنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
«إِذَا شَرِبَ الْكَلْبُ فِي إِنَاءِ أَحَدِكُمْ فَلْيَغْسِلْهُ سَبْعًا».
ولمسلم: « أولاهُنَّ بالتُراب».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 172]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 172]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da wanke kwarya sau bakwai idan kare ya shigar da harshensa a cikinta, na farko daga cikinsu a haɗa da turbaya sai ruwa ya biyo bayanta, sai cikakkiyar tsafta ta tabbata daga najasarsa da kuma cutarsa.