عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُكْثِرُ أَنْ يَقُولَ: «يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، آمَنَّا بِكَ وَبِمَا جِئْتَ بِهِ فَهَلْ تَخَافُ عَلَيْنَا؟ قَالَ: «نَعَمْ، إِنَّ القُلُوبَ بَيْنَ أُصْبُعَيْنِ مِنْ أَصَابِعِ اللهِ يُقَلِّبُهَا كَيْفَ يَشَاءُ».
[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 2140]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa" sai na ce: Ya Manzon Allah, mun yi imani da kai da kuma abinda ka zo da shi, shin kana jin tsoro akanmu ne? ya ce: "Eh, lallai zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana jujjuyasu yadda Ya ga dama".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 2140]
Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance rokon Allah ne tabbata akan addini da biyayya, da nisanta daga karkata da kuma bata, Sai Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamakin yawaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wannan addu'ar, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi labarin cewa zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana juyasu yadda Ya ga dama, Zuciya ita ce gurin imani da kafirci, hakika an anbaci zuciya (Kalbu) saboda yawan jujjuawarta; ita ce mafi tsananin jujjuyawa daga tukunya idan ta tafarfasa, wanda Allah Ya so Zai tsaida zuciyarsa akan shiriya, ya tabbatar da shi akan addini, wanda Allah Ya ga dama kuma Zai juyar da zuciyarsa daga shiriya zuwa karkata da bata.