عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ نَسِيَ وَهُوَ صَائِمٌ، فَأَكَلَ أَوْ شَرِبَ، فَلْيُتِمَّ صَوْمَهُ، فَإِنَّمَا أَطْعَمَهُ اللهُ وَسَقَاهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1155]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne Ya ciyar da shi kuma Ya shayar da shi".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1155]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa alhali shi yana cikin azimin farilla ko nafila to ya cika aziminsa kada ya karya; domin cewa shi bai yi nufin karyawa ba, kawai shi wani arziƙi ne Allah Ya koro masa kuma Ya ciyar da shi Ya shayar da shi.