+ -

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: «كان رسول الله صلى الله عليه وسلم في سفر. فَرَأَى زِحَامًا وَرَجُلًا قد ظُلِّلَ عليه، فقال: ما هذا؟ قالوا: صائم. قال: لَيْسَ مِنَ البِرِّ الصِّيَامُ فِي السَّفَرِ»، وفي لفظ لمسلم: « عَلَيْكُمْ بِرُخْصَةِ الله الَّذِي رَخَّصَ لكم».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jabir dan abdullahi-Allah yarda da shi- ya ce: "Annabi ya kasance a cikin tafiya sai yaga taron mutane sunyi wa wani inuwa, sai ya ce: Maye wannan? sai suka ce Azumi yake sai ya ce: "Baya daga cikin bin Allah Azumi a cikin tafiya" kuma a cikin wani Lafazin na Muslim: "Na horeku da saukin da Allah ya saukake muku da shi"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Jabir yana bamu labarin cewa Annabi ya kasance a cikin Tafiyarsa ta shekarar Bude Makka sai yaga Wani Mutum anyimasa Inuwa gashi kwance, kamar yadda yake a cikin riwayar Hadisin Dan Jarir, sai ya tambaye su lamarinsa sai suka c: Cewa shi Azumi yake yikuma kishirwa ta cimmasa haka. to sai Annabi ya ce: "lallai cewa Azumi a halain tafiya baya cikin Bin Allah, kuma sai dai na hore ku da saukin da Allah yayi muku, kuma shi bai nufi kuyi Ibadarsa ba ta hanyar Azabtar da kawunanku. Taisir Allam(shafi na327) Tanbih Al'afham (3/44) Ta'asis Al'ahkam 3/244

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin