عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: كان النبي صلى الله عليه وسلم يعتكف في كل رمضان عشرة أيام، فلما كان العام الذي قُبِضَ فيه اعتكف عشرين يوماً.  
                        
[صحيح] - [رواه البخاري]
                        
 المزيــد ... 
                    
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Manzon Allah SAW ya Kasance yana E'itikafi a cikin goman kowane Azumin Ramadan, to yayin da shekarar da aka karbi ransa ta zo yayi E'itikafi kwana Ashirin" 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi]                                            
Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana laamtara Masallaci yana yanke komai ya koma ga Allah cikin kwana goma na Azumi, kuma yanayi E’itikafi a cikin goman tsakiyarsa; don fatan riskar daren lalatulkadari yayin da aka san cewa tana goman Karshe ne na watan, sannan yayi E’itikafi a Shekarar day a yi wafati a ciki kwana Ashirin don Karin biyayya; don kusantara Allah Madaukakin Sarki