+ -

عَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«يَا أَبَا ذَرٍّ إِذَا طَبَخْتَ مَرَقَةً فَأَكْثِرْ مَاءَهَا، وَتَعَاهَدْ جِيرَانَكَ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2625]
المزيــد ...

Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ya Abu Zarr idan zaka dafa romo to ka yawaita ruwansa, ka bibiyi maƙotanka da shi".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2625]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitarwa Abu Zarr al-Gifari - Allah Ya yarda da shi - cewa idan zai dafa romo to ya yawaita ruwansa, ya bibiyi maƙotansa da shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan kyakkyawar mu'amala tare da maƙota.
  2. An so yin kyauta tsakanin maƙota; domin hakan yana gadar da soyayya kuma yana ƙara ƙauna, wannan kyautar tana ƙarfafuwa idan abincin yana da ƙanshi, kuma an san buƙatuwar maƙoci (gare shi).
  3. Kwaɗaitarwa akan bada abin alheri da abinda ya sawwaƙa daga gare shi koda kaɗan ne, da shigar da farin ciki ga musulmai.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin