عَنْ أَبِي شُرَيْحٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ، وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ، وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ»، قِيلَ: وَمَنْ يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ قَالَ: «الَّذِي لاَ يَأْمَنُ جَارُهُ بَوَايِقَهُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6016]
المزيــد ...
Daga Abu Shuraih - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa».
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6016]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa kuma ya ƙarfafi rantsuwarsa sau uku, sai ya ce: Wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, sai sahabbai suka tambaye shi : Waye wanda ba mumini ba ya Manzon Allah? ya ce: Wanda maƙocinsa yake jin tsoron yaudararsa da zalincinsa da kuma sharrinsa.