1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Duk wanda ba ya godewa mutane to ba zai godewa Allah ba

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا يَشْكُرُ اللَّهَ مَنْ لَا يَشْكُرُ النَّاسَ»

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Duk wanda ba ya godewa mutane to ba zai godewa Allah ba".

Ingantacce ne Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad Sunan Abi Dawud - 4811

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duk wanda a al'adarsa ba ya godewa mutane akan alheri da abu mai kyau da suka yi masa to ba zai godewa Allah ba, hakan dan haduwar al'amura biyun da ɗaya, domin wanda daga cikin ɗabi'arsa da al'adarsa ita ce butulcewa ni'imar mutane da barin gode musu, to al'adarsa zata zama butulcewa ni'imar Allah da kuma kasawa a gode maSa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Muhimmancin godewa mutane akan aikin laheri.
  2. Mai ni'imtarwa a haƙiƙa shine Allah - Maɗaukakin sarki -, ɗabi'u sabubba ne waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Yake horesu ga wanda Yake so, saboda haka ne lallai cewa godewa mutane yana daga cikin gode wa Allah - Maɗaukakin sarki -.
  3. Godewa mutane akan aikin alherinsu dalili ne akan cikar ɗabi'u.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ID Indonesia الإندونيسية
BN বাংলা البنغالية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
TH ไทย التايلندية
AS অসমীয়া الأسامية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية