+ -

عن ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَيُّمَا امْرِئٍ قَالَ لِأَخِيهِ: يَا كَافِرُ، فَقَدْ بَاءَ بِهَا أَحَدُهُمَا، إِنْ كَانَ كَمَا قَالَ، وَإِلَّا رَجَعَتْ عَلَيْهِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 60]
المزيــد ...

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 60]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar da musulmi ya ce wa ɗan'uwansa musulmi: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya cancanci kalmar kafircin, idan ya kasance kamar yadda ya faɗa ne, inba haka ba kafirtawar da ya yi wa ɗan'uwansa za ta dawowa wanda ya fada.

Fassara: Turanci Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tsawatarwa musulmi akan ya faɗawa ɗan'uwansa musulmi abinda babu a cikinsa na siffofin fasiƙanci da kuma kafirci.
  2. Gargaɗarwa daga wannan mummunar maganar, kuma cewa mai ita yana kan haɗari mai girma idan ya faɗeta ga ɗan'uwansa, to yana kamata kiyaye harshe kuma kada ya yi magana sai da tunani.