+ -

عَنْ مَالِكِ بْنِ أَوْسِ بْنِ الْحَدَثَانِ أَنَّهُ قَالَ: أَقْبَلْتُ أَقُولُ مَنْ يَصْطَرِفُ الدَّرَاهِمَ؟ فَقَالَ طَلْحَةُ بْنُ عُبَيْدِ اللهِ وَهُوَ عِنْدَ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ رضي الله عنهما: أَرِنَا ذَهَبَكَ، ثُمَّ ائْتِنَا، إِذَا جَاءَ خَادِمُنَا، نُعْطِكَ وَرِقَكَ، فَقَالَ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ: كَلَّا، وَاللهِ لَتُعْطِيَنَّهُ وَرِقَهُ، أَوْ لَتَرُدَّنَّ إِلَيْهِ ذَهَبَهُ، فَإِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«الْوَرِقُ بِالذَّهَبِ رِبًا، إِلَّا هَاءَ وَهَاءَ، وَالْبُرُّ بِالْبُرِّ رِبًا، إِلَّا هَاءَ وَهَاءَ، وَالشَّعِيرُ بِالشَّعِيرِ رِبًا، إِلَّا هَاءَ وَهَاءَ، وَالتَّمْرُ بِالتَّمْرِ رِبًا، إِلَّا هَاءَ وَهَاءَ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1586]
المزيــد ...

Daga Malik ɗan Aus ɗan Hadasan cewa shi ya ce: Na taho ina cewa waye zai canji dirhamomi? sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi alhali shi yana wurin Umar ɗan Khaɗɗab - Allah ya yarda da su - ya ce: Ka nuna mana zinarenka, sannan kazo mana, idan ɗan aikinmu ya zo, zamu baka azirfarka, sai Umar ɗan Khaɗɗab ya ce: A'a, wallahi kodai ka ba shi azirfarsa, ko ka dawo masa da zinarensa, domin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Azirfa da zinare riba ne, sai hannu da hannu, alkama da alkama riba ne, sai hannu da hannu, sha'ir da sha'ir riba ne, sai hannu da hannu, dabino da dabino riba ne, sai hannu da hannu".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1586]

Bayani

Tabi'i Malik ɗan Aus yana bada labari cewa shi ya kasance a wurinsa akwai zinarai, kuma yana son ya canja su da azirfofi, sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce masa: Ka bamu zinarenka dan na gansu! sannan ya ce da shi bayan ya yanke zai saya: Ka je Ka dawo, idan ɗan aikinmu ya zo bayannan dan mu baka dirhamomin, Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana halarce a wurin, sai ya yi inkarin wannan nau'in na mu'amala, kuma ya yi wa Ɗalha rantsuwa akan cewa ya bada azirfar a take, ko ya dawo masa da zinarensa wanda ya karba daga gare shi, kuma ya bayyana masa sababin hakan cewa Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa saida zinari da azirfa ko akasin hakan ya wajaba ya zama hannu da hannu nan take, inba haka bafa to wannan cinikin zai zama riba abin haramtawa, kuma bataccen ciniki, ba'a saida zinari da azirfa ko azirfa da zinari sai hanuu da hannu kuma karba ya tabbata, haka ba'a saida alkama da alkama ko wake da wake ko sha'ir da sha'ir ko dabino da dabino sai daidai wa daidaida awo da awo,

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الرومانية Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Nau’ukan da aka ambata a cikin wannan hadisin guda biyar ne: Zinare da azirfa da alkama da wake da sha'ir da dabino, idan ciniki ya tabbata a su sinfin to babu makawa dan inagancin cinikin daga sharuɗɗa biyu: Karɓa a majalasin ƙulla cinikin, da kuma daidaito a awo, kamar zinare da zinare, inba haka bafa zai zama riba ta fifiko, idan sun saɓa kamar azirfa da alkama misali to sharaɗi ɗaya ne dan ingancin ƙulla cinikin, shi ne karɓar kuɗin a majalasin ƙulla cinikin, inba haka bafa zai zama riba ta jinkiri.
  2. Ana nufi da majalasin ƙulla ciniki: Gurin ciniki, daidai ne sun kasance a zaune, ko suna tafiya, ko akan abin hawa, kuma ana nufi da rabuwa abinda ake ɗauka a matsayin rabuwa a al'ada tsakaknin mutane.
  3. Hani a cikin hadisin ya ƙunshi dukkan nau'ikan zinaren da aka kera da wasunsu, da kuma dukkan azirfar da aka kera da wacce ba'a kera ba.
  4. Takardun kudade a wannan zamanin yana tabbata a cikinsu abinda yake tabbata acikin saida zinare da a zirfa, wato idan ka yi nufin canja wani kuɗi da wani kuɗin daban kamar riyal da dirhami to fifiko ya halatta da abinda masu ƙulla cinikin suka yarda da shi, sai dai karɓa yana wajaba a wurin siyarwar, inba haka ba to cinikin ya ɓaci, mu'amalar ta zama riba wacce haramta.
  5. Mu'amaloli na riba basa halatta, kuma ƙullasu ɓatacce ne koda masu cinikin sun yarda; domin Musulunci yana kiyaye haƙƙin mutum da haƙƙin zamantakewa koda shi ya haƙura na shi.
  6. Hani daga abin ƙi da kuma hana shi ga wanda zai iya hakan.
  7. Anbatan dalili a lokacin inkarin abin ƙi, kamar yadda Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya yi.