عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«الذَّهَبُ بِالذَّهَبِ، وَالْفِضَّةُ بِالْفِضَّةِ، وَالْبُرُّ بِالْبُرِّ، وَالشَّعِيرُ بِالشَّعِيرِ، وَالتَّمْرُ بِالتَّمْرِ، وَالْمِلْحُ بِالْمِلْحِ، مِثْلًا بِمِثْلٍ، سَوَاءً بِسَوَاءٍ، يَدًا بِيَدٍ، فَإِذَا اخْتَلَفَتْ هَذِهِ الْأَصْنَافُ، فَبِيعُوا كَيْفَ شِئْتُمْ، إِذَا كَانَ يَدًا بِيَدٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1587]
المزيــد ...
Daga Ubadah ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1587]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana hanyar yin inagntaccen ciniki a cikin nau’ukan da riba take shiga cikinsu (abubuwa) guda shida sune: Zinare, da azirfa, da alkama, da sha'ir, da dabino, da gishiri, idan sun kasance daga irin nau'in ne kamar saida zinare da zinare azirfa da azirfa... to babu makawa daga sharuɗɗa biyu: Na farko: Tabbatar daidaituwa a cikin awon sikeli ne, idan ya kasance abin aunawa ne na sikeli kamar zinare da azirfa, ko samun daidaito a awo idan ya kasance abin aunawa ne na kwano kamar alkama da sha'ir da dabino da kuma gishiri. Na biyu: Mai siyen ya karɓi abin siyarwar shi kuma mai siyarwar ya karɓi kuɗin, hakan (ya zama) a gurin da akayi cinikin. Idan waɗannan nau’ukan suka saɓa kamar saida zinare a bada azirfa, da dabino a bada alkama misali, to cinikin ya halatta da sharaɗi ɗaya, shi ne mai siyarwar ya karɓi kuɗin shi kuma mai siyen ya karɓi abin siyan a gurin da aka yi cinikin, inba haka bafa to cinikin ɓatacce ne, kuma sun faɗa cikin ribar da aka haramta, mai siyen da mai siyarwar duk ɗaya ne a hakan.