عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا أَسْفَلَ مِنَ الكَعْبَيْنِ مِنَ الإِزَارِ فَفِي النَّارِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 5787]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Duk mayafin da ya yi ƙasa da idan sawu to yana cikin wuta".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5787]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi maza daga sakin dukkan abinda yake suturce jikinsu tufa ne ko wanduna ko waninsu ƙasa da idan sawun diga-digai, kuma abinda ke ƙasan idan sawu na ƙafar mai mayafin da ya sake shi to shi yana cikin wuta dan yi masa uƙuba akan aikinsa.