عن أبي هريرة رضي الله عنه قال:
لعن رسول الله صلى الله عليه وسلم الرجل يلبس لِبْسَةَ المرأة، والمرأة تلبس لِبْسَةَ الرجل.
[صحيح] - [رواه النسائي في الكبرى وابن ماجه بمعناه وأحمد] - [السنن الكبرى للنسائي: 9209]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji.
[Ingantacce ne] - - [السنن الكبرى للنسائي - 9209]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah ga dukkan namijin da ya yi kama da mace a cikin tufafin da suka keɓanci mata; daidai ne a cikin kama ne ko launi ko kaifiyya ko hanyar sanyawa da ado ko wanin haka. Ko mace ta yi kama da kayan da suka keɓanci maza kamar haka, kuma shi laifi ne babba daga manyan laifuka.