+ -

عن ابنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم:
«مَن تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ».

[حسن] - [رواه أبو داود وأحمد] - [سنن أبي داود: 4031]
المزيــد ...

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu".

[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 4031]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane daga kafirai ko fasiƙai ko mutanen kirki - ta yadda zai aikata wani abu daga abin da ya keɓancesu daga aƙidu ko ibadu - to, yana daga cikinsu; domin kamanceceniya da su a zahiri yana kaiwa zuwa kamanceceniya da su a ɓoye, kuma babu kokwanto cewa kamanceceniya da mutane yana haifuwa ne daga sha'awarsu, kuma ya kan kai zuwa ga soyayyarsu da girmamasu da karkata zuwa garesu, wannan yana jan mutum zuwa ya yi kama da su har a ɓoye da ibada - Allah Ya yi mana tsari-.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Gargaɗi daga kamanceceniya da kafirai da fasikai.
  2. Kwaɗaitarwa a kan kamanceceniya da mutanen kirki da koyi da su.
  3. Kamanceceniya a zahiri yana gadar da soyayya a ɓoye.
  4. Mutum yana samun narko da zunubi gwargwadon kamanceceniya da nau'inta.
  5. Hani daga kamanceceniya da kafirai a addininsu da al'adunsu waɗanda suka keɓanta da su, amma abin da bai zama irin hakan ba kamar neman sanin sana'o'i da makamancinsu, to, ba ya shiga a cikin hanin.