عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَتَتَّبِعُنَّ سَنَنَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ، شِبْرًا بِشِبْرٍ، وَذِرَاعًا بِذِرَاعٍ، حَتَّى لَوْ دَخَلُوا فِي جُحْرِ ضَبٍّ لَاتَّبَعْتُمُوهُمْ» قُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ آلْيَهُودَ وَالنَّصَارَى؟ قَالَ: «فَمَنْ؟».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2669]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i, har da ko sun shiga ramin damo ne sai kun bi su" Muka ce: Ya manzon Allah ! Yahudawa da Nasara? ya ce: "To su wa?".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2669]
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana bada labarin abinda halin da sashin al'ummarsa zasu kasance akansa bayan zamaninsa, shi ne bin hanyar Yahudawa da Nasara a aƙidunsu da ayyukansu da al'adunsu bi na zirfafawa mai tsanani taki da taki, zira'i da zira'i, har da a ce su shiga ramin damo to da waɗannan zasu shige shi suna bayansu.