عَن أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا يَنْظُرُ الرَّجُلُ إِلَى عَوْرَةِ الرَّجُلِ، وَلَا الْمَرْأَةُ إِلَى عَوْرَةِ الْمَرْأَةِ، وَلَا يُفْضِي الرَّجُلُ إِلَى الرَّجُلِ فِي ثَوْبٍ وَاحِدٍ، وَلَا تُفْضِي الْمَرْأَةُ إِلَى الْمَرْأَةِ فِي الثَّوْبِ الْوَاحِدِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 338]
المزيــد ...
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace, kuma kada wani namiji ya lulluɓa da wani mutum a cikin mayafi ɗaya, kuma kada wata mace ta lullaɓa da wata mace cikin mayafi ɗaya".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 338]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana namiji ya kalli al'aurar namiji, ko mace ta kalli al'aurara mace.
Al'aura: Ita ce dukkanin abinda ake jin kunya daga gareshi idan ya bayyana, al'aurar namiji ita ce tsakanin cibiyarsa da gwiwoyinsa, mace dukkaninta al'aurace dangane da maza na nesa, (wadanda akwai aure a tsakanin su) dangane da mata kuwa ko maharramanta to ita zata bayyanar da abinda yake bayyana a al'adance a lokacin aikinta a cikin gida.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga kaɗaituwar namiji da namiji a tufafi ɗaya , ko ƙarƙashin mayafi ɗaya alhali suna cikin tsiraici, da kuma mace ta kaɗaita da mace a tufafi ɗaya ko ƙarƙashin mayafi ɗaya a tsiraice; Domin hakan zai iya kaiwa zuwa shafar al'aurar kowanne daga garesu, shafarta kuwa abin hanawa ne, kamar kallon al’amuran ne, kai shi ne ma mafi tsanani a hani; Saboda hakan zai iya kaiwa zuwa barna girma.