+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«صِنْفَانِ مِنْ أَهْلِ النَّارِ لَمْ أَرَهُمَا، قَوْمٌ مَعَهُمْ سِيَاطٌ كَأَذْنَابِ الْبَقَرِ يَضْرِبُونَ بِهَا النَّاسَ، وَنِسَاءٌ كَاسِيَاتٌ عَارِيَاتٌ مُمِيلَاتٌ مَائِلَاتٌ، رُؤُوسُهُنَّ كَأَسْنِمَةِ الْبُخْتِ الْمَائِلَةِ، لَا يَدْخُلْنَ الْجَنَّةَ، وَلَا يَجِدْنَ رِيحَهَا، وَإِنَّ رِيحَهَا لَيُوجَدُ مِنْ مَسِيرَةِ كَذَا وَكَذَا».

[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Nau'i biyu daga 'yan wuta ban gan su ba; Wasu mutane atare da su akwai bulalai kamar jelunan shanu suna dukan mutane da su. Da wasu mata masu sanye da tufafi kuma tsirara masu jawo hankula kuma karkatattu, kawunansu kamar tozan muturu ne mai karkacewa, ba za su shiga aljanna ba, kuma ba za su ji ƙanshinta ba, kuma cewa ƙanshinta ana samunsa daga tafiyar kaza da kaza".

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana gargaɗI akan nau'i biyu daga mutane cikin 'yan wuta bai gan su ba, kuma ba'a samesu a zamaninsa ba, kawai za su kasance ne a bayansa:
Nau'i na farko: Wasu mutane ne a tare dasu akwai bulalai kamar jelunan (bidin) shanu masu tsawo, suna dukan mutane da su, sune 'yan sanda da mataimakan azzalumai waɗanda suke dukan mutane ba tare da wani haƙƙi ba.
Nau'i na biyu: Wasu mata ne da suka cire tufafin kamewa da kunya wanda aka ɗabi'anci mace akansa a al'adan ce.
Shi Siffantasu da: Masu sanye da tufafi a haƙiƙa, matsiraita a ma'ana; Domin cewa su suna sanye da taufafi shara-shara yana nuna fatar jiki, kuma suna suturce wani abu daga jikinsu suna yaye sashinsa; dan bayyanar da kyaawunsu. masu karkato da zuciyar maza zuwa garesu , saboda tufafin da suka saka, da taƙamarsu a tafiya, masu karkatar da kafaɗunsu, kuma suna karkato da wasunsu zuwa karkacan tunani da bata wanda suka afkawa a cikinsa, Daga siffofinsu: Kawunansu tamkar tozon karkataccen raƙumi ne, suna kuma kara girman kawunan nasu, suna ƙara masa girma ta hanyar rufa masa kari da waninsa, Kamanta su da aka yi da tozon aturkumami kawai dan dago gashinsu ne da faratansu a saman kawunansu, da karairayarsu da abinda zai kitsantar da shi har ya karkace zuwa wani ɓangare daga ɓangarorin kai, kamar yadda tozon raɗumi yake karkacewa. Duk waɗanda suka kasance da waɗan nan siffofin to a tare da su akwai wannan narkon mai tsanani cewa ba za su shiga aljanna ba kuma ba za su ji ƙanshinta ba kuma ba za su yi kusa da ita ba, kuma ƙanshin aljanna ana samunsa ana shaƙarsa daga tafiya mai nisa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin dukan mutane ba tare da wani laifin da suka aikata ba, kuma ba tare da laifin da da suka aikata shi.
  2. Haramcin taimakawa azzalumai akan zalincinsu.
  3. Gargaɗin mata daga shigar tsiraici da sanya tufafi ƙuntatacce mai shara-shara wanda yake siffanta al'aura ko yake bayyana jikinta.
  4. Kwaɗaitar da mace musulma akan lazimtar umarnin Allah, da nisanta daga abinda zai sa Shi fushi, ya sanaya ta ta canacanci azaba mai raɗadi madawwamiya a lahira.
  5. Hadisin yana daga dalilan Annabta ta tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, yayin da tsira da aminci su tabbata agare shi ya bada labari game da al'amura ɓoyayyu waɗanda ba su faru ba, kuma suka faru kamar yadda ya bada labari.