عَنْ جَرِيرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
سَأَلْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ نَظَرِ الْفُجَاءَةِ فَأَمَرَنِي أَنْ أَصْرِفَ بَصَرِي.  
                        
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2159]
                        
 المزيــد ... 
                    
Daga Jariri ɗan Abadullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da gani na fuj'a sai ya umarceni in juyar da ido na. 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2159]                                            
Jarir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ganin da namiji zai yi wa mace manisanciyarsa bagtatan ba tare da nufi ba? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce shi cewa ya wajaba agare shi ya juyar da fuskarsa zuwa wani ɓangaren da wata nahiyar daban da zarar ya sani, babu laifi akansa.